Tsohon alkali ya tsallake rijiya da baya daga masu garkuwa

0

A ranar Litini ne da misalin karfe tara na yamma wasu masu garkuwa da mutane suka nemi sace tsohon alkalin kotun daukaka kara kuma hakimin Malumfashi Mamman Nasir.

Mazauna garin Malumfashi sun bayyana wa manema labarai cewa masu garkuwan sun yi kokarin sace Nasir ne a hanyar dake kusa da kauyukan Gora da Yamamama dake karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina.

Nasir ya tsallake rijiya da baya ne a dalilin gaggauta ficewa daga cikin motar da yake ciki tare da mai tsaron sa wato Aminu bayan ya hango masu garkuwa na tsaida motoci a wannan hanya.

Sai dai shi Amimu bai sami sa’ar da Nasir ya samu ba domin sun yi ram da shi suka tafi da shi tare da sauran matafiya da suka tattara.

Mutane da dama na ta zuwa gidan Hakimi Nasir domin yi masa jaje.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar bata ce komai ba.

Share.

game da Author