Shugaban hukumar tara haraji na jihar Kaduna Muktar Ahmed ya bayyana cewa a cikin shekara uku hukumar ta tara harajin Naira biliyan 91.2.
Ahmed ya fadi haka ne ranar Litini a Kaduna a taron gabatar da aiyukkan da hukumar ta yi na shekara uku da suka gabata.
Ya ce KDIRS ta sami nasarar yin haka ne a dalilin gyara da wannan gwamnatin ta yi na wajen tsara yadda za ana rika karba da tara haraji da kashi 30 bisa 100.
” A 2015 KDIRS ta tara harajin Naira biliyan 11.8 wannan kudi kuwa ya karu zuwa Naira biliyan 23.5 a 2016 daga nan ya zama biliyan 26.7 a 2017 sannan kuwa yanzu mun tara Naira biliyan 29.4 a 2018.
” Gyaran da wannan gwamnati ta yi sun hada da toshe kafofin da akan rika amfani da su wajen wawushe kudade da hukumar ta dade tana fama da su, karin ma’aikata, horar da ma’aikata, inganta yin rajistan ababen hawa da makamantan su.
A karshe Ahmed ya ce hukumar ta bude ofisoshin karban haraji a duk kananan hukumomin dake jihar sannan a cikin wadannan ofisoshin a kwai fannin sauraron kararraki daga wurin mutane.
Discussion about this post