ONNOGHEN: Majalisar Alkalai (NJC) da Kungiyar Lauyoyi (NBA) za su yi zama na musamman

0

Majalisar Alkali ta Kasa (NJC) da kuma Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA), za su yi zama na musamman kuma na gaggawa, domin tattauna dakatarwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen.

An dakatar da Onnoghen ranar Juma’a bisa umarnin Kotun CCT, matakin da ‘yan Najeriya da kasashen Turai da Amurka suka yi wa Allah wadai.
Jiya Lahadi ne NJC da NBA suka bayyana cewa za su yi ganawa ta musamman a ranakun Litinin da Talata.

Yayin da taron da NJC za ta yi ba a bayyana shi a fili, ba, amma dai wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa za a yi taron na gaggwa, shi kuwa taron da NBA za su yi, tuni an sanar da hakan ta bakin wata sanarwa da Babban Sakataren Kungiyar ta Lauyoyi, Jonathan Taidi ya sa wa hannu.

NJI za su yi na su taron, sannan kuma majiya ta ce ba dakataccen Cif Joji ko kuma sabon ne zai shugabanci zaman ba.

A na ta bangaren, NBA za ta gaba ne, kuma ta gayyaci dukkan Shugabannin Kungiyar na yanzu, dukkan shugabbanin kungiyar da suka gabata wadanda ke raye, kuma an gayyaci tsoffin sakatarori da shugabanni na jihohi, na da da na yanzu.

NBA dai ba ta yarda da dakatar da Onnoghen ba.

Majalisar Alkali ta Kasa ma in banda mutum daya daga cikin mambobi 16, babu wanda ya halarci taron rantsar da sabbin alkalan shari’un kararrakin zabe da sabon Cif Joji ya rantsar a ranar Asabar.

Share.

game da Author