ZAMA DA MADAUKIN KANWA: Abacha malamin Buhari ne, kuma Buhari ya karantu da kyau – Inji Atiku

0

Dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa kusancin Abacha da Buhari ne ya sa ya ke taka kowa ya yi abinda ya ga dama ba tare da ya bi dokar wajen yanke hukunci a abubuwan da ya shafi kasa Najeriya ba.

” Idan ba a manta ba da rana tsaka Abacha ya tsige sarkin Musulmi a lokacin da ya ke shugaban kasar nan kuma sanin kowa ne cewa Buhari dan gaban goshin sa ne suna tare ya aikata haka. Ka ga ko ay ya karantu sosai da yadda ake karya doka daga wajen malamin sa Abacha.” Inji Atiku.

Atiku ya kara da cewa abinda da yafi tada masa hankali shine yadda kiri-kiri shugaba Buhari ya taka doka sannan yayi rugu-rugu da ita don ya cimma burin sa. Atiku ya ce ba yana wage baki don mara wa Walter Onnoghen baya bane.” Dole mu fito mu fadi gaskiya a inda aka saba wa dokar kasa sannan mu fadi gaskiya komai dacin ta.

” Idan sun afka wa shugabannin majalisar kasa, mun yi shiru saboda mu ba wakilai bane a majalisa, suka kai wa gidajen jaridun kasa hare-hare muka tsuke baki saboda mu ba ‘yan jarida bane, suka fada wa bangaren shari’a muka yi shiru wata rana zasu afko mana babu wanda zai cece mu.

Duka da tofa albakacin baki da mutane suka rika yi na yin tir da dakatar da Onnoghen da Buhari ya yi, fadar shugaban kasa ta kafe cewa babu inda ta saba wa dokar kasa a abinda ta yi.

Sannan kuma ta maida wa Amurka da kungiyar tarayyar Turai da martani bisa yin suka ga dakatar da Alkali Onnoghen.

Cikin sanarwar da Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar, duk da cewa Najeriya na neman hadin kan Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai wajen tabbatar da cewa an gudanar da zaben 2019 cikin adalci da kwanciyar hankali, to kuma ba za ta lamunci wasu kasashe su rika yi mata katsalandan a harkokin da suka shafi cikin gida Najeriya ba.

Share.

game da Author