Gwamnati za ta gindaya sharuddan kwasa da zuba kudade a Asusun Rarar Man Fetur

0

Kwamitin Gwamnatin Tarayya mai lura da Kasafta Kudaden Tarayya ya fara tunanin gindaya sharuddan da gwamnati za ta gindaya kafin a rika kwasar kudade daga Asusun Rarar Ribar Danyen Man Fetur, wanda aka fi sani da ‘Excess Crude Account’ (ECA).

Wadannan sharudda kwamiti ne wanda aka kafa tun cikin watan Yuli, 2018 ya bijiro da su.

Sharudda na farko su ne, a duk wata kada kudaden da tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi ke kashewa su kasa kai naira bilyan 680.

Sharadi na biyu shi ne, ba za a zabtarar kudade daga Asusun Rarar Mai ba, sai idan kudaden ba su kai naira bilyan 680 da za a raba ba, sannan za a ciro daga ECA.

Sharadi na uku shi ne, idan ribar mai da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi za su raba a karshen wata, har ta zarce naira bilyan 680 zuwa 730, to za a kwashi naira bilyan 50 a zuba cikin Asusun Rarar Mai, ECA.

Sharadi na 4, idan ribar ta kai naira bilyan 730 zuwa bilyan 830, to za a kwashi naira bilyan 100 a adana cikin ECA.

Sharadi na 5, idan ribar kudaden ta kai naira bliyan 830 abin da yay i zama, to za a cire naira bilyan 150 a adana cikin Asusun ECA, saura kuma gwamnatocin su kasafta a tsakanin su.

Sharadi na 6: Kada a kara cirar wasu kudade daga cikin kason kashi 13 bisa 100 da ake tara wa jihohin da ke da arzikin danyen man fetur a kasar nan.

Sharadi na 7: A duk karshen wata a rika lissafa adadin kashi 13 na rarar ribar danyen mai, ana tura wa asusun jihohin da ke da arzikin danyen mai kai-tsaye ba tare da bata lokaci ba.

Asusun ECA, wani dadadden asusu ne da gwamnatin tarayya ta kafa, wanda ake tara rarar kudaden ribar danyen man fetur man fetur da ake saidawa sama da farashin da gwamnatin tarayya ta yi kintacen farashin sa a kasafin kudi.

Gwamnonin jihohi masu arzikin danyen man fetur ne a cikin 2018 suka tayar da kayar-bayan cewa sun gaji da yadda gwamnatin tarayya ke yawan wasgar kudade daga Asusun ECA, wanda ake tara kudaden da ake ba su na kashi 13 bisa 100.

Share.

game da Author