Kiraye-kiraye, caccaka da Allah-wadai bai sa sojoji sun saki editan Daily Trust ba

0

Duk da tsananin kiraye-kiraye, caccaka da Allah-wadai bai sa sojoji sun saki editan Daily Trust ba.

Har zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari, mahukuntan sojojin Najeriya na tsare da editan shiyyar Arewa maso Gabas na jaridar Daily Trust, Usman Abubakar.

An kama Abubakar tun a ranar Lahadi a Maiduguri, jihar Barno tare da daya daga cikin dan rahoton jaridar mai suna Ibrahim Sawab, a wani samame da suka kai ofishin jaridar.

Bayan nan ne sojoji suka mamaye ofishin Trust da ke Abuja, tare da kwashe kwamfutoci masu dama.

Bayan an yi ta yin Allah-wadai da abin da sojoji suka aikata, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin sojoji su gaggauta ficewa daga gidan jaridar.

Amma a ranar Ladi da misalin 10 na dare, sojoji sun saki Sawab, amma suka ci gaba da rike Usman Abubakar.

Sawab ya shaida cewa sojoji sun damka Abubakar a hannun jami’an SSS domin yi masa tambayoyi.

Abubakar dai kamar yadda Sawab ya bayyana, ya na fama da matsalar rashin lafiya, gashi kuma shekarun sa sun kai 55. Dama kuma a kullum cikin yanayi na shan magani ya ke.

Share.

game da Author