El-Kanemi Warriors ta lallasa Kano Pillars da 2-1

0

A yau Alhamis ne kungiyar Kwallon kafa ta El-Kanemi Warriors ta lallasa takwarar ta Kano Pillars da ci 2 da 1.

Kano Pillars ce ta fara zura wa El-Kanemi kwallo a raga ta hannun dan wasan ta Bello Kofarmata a daidai ana minti 20 da fara wasa. Ali Rabiu na El-Kanemi ya ramo cin a minti 45.

A daidai minti 71 sai Razak Aliyu ya zura kwallo ta biyu a ragar Pillars.

An ba Bello Kofarmata jan kati ana saura minti hudu a tashi wasa inda Pillars suka gama wasa da yan wasa 10.

Bisa wannan nasara da El-Kanemi ta samu, ita ce a saman tebur in da Pillars ke na biyar da maki 3 a wasa biyu da ta buga.

Kungiyoyin Kada city, Yobe Desert Stars da Gombe United ba su buga wasa ko daya aba tukunna.

Share.

game da Author