Hukumar Kwallon Najeriya ta ci kungiyar Plateau United tara mai tsanani

0

A jiya Laraba ne Hukumar Shirya Gasar Kwallon Kafa ta Najeriya ta haramta wa kungiyar Plateau United buga kwallo a garin Jos har na tsawon wasanni uku.

Sauran tarar da aka ci kungiyar sun hada da biyan tsabar kudi har naira miliyan 5.

An ci kungiyar tara ne sakamakon cin zarafin alkalan wasa da aka yi a filin kwallon Jos, a lokacin da Plateau United, mai masaukin baki, ta yi canjaras da Ifeanyi Ubah FC.

An yi wasan ne a ranar Asabar da ta gabata.

An ce wani mai goyon bayan kungiyar mai suna Attahiru Babayo ya ja zugar wadanda suka afka cikin fili suka ci zarafin alkalan wasan.

A kan haka ne aka yanke cewa Plateau United za ta yi wasannin ta uku na gaba a garin Ilorin.

Sannan kuma an umarci jami’an kulob din cewa su mika Babayo wurin jami’an tsaro, ko kuma a kullum za a ci su tarar naira 25,000, har sai ranar da aka kamo shi.

Jami’in hukumar mai suna Salihu Abubakar, ya gargadi Plateau United cewa idan aka kara tayar da hargitsi a filin kwallon Jos, to a za cire wa kungiyar maki uku kai-tsaye.

‘Yan kallo sun yi korafin cewa an nuna wa Plateau United son kai a wasan, wanda wannan ne ya fusata magoya bayan ta.

Share.

game da Author