BULLOWAR ZAZZABIN LASSA: Matakan da muka dauka wajen ganin mun dakile yaduwar cutar – NCDC

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ta bayyan cewa ta dauki wasu matakai domin ganin an dakile yaduwar zazzabin lasa da ya bullo gadan-gadan.

NCDC ta fadi haka ne bayan sanar da bullowar cutar a kasar da ta yi ranar Talata.

Hukumar ta ce sakamakon binciken da ta gudanar a watan Janairu ya nuna cewa mutane 60 na dauke da cutar a jihohi takwas a kasar nan.

“Mun kuma gano cewa mutane kan yi fama da matsaloli da dama a dalilin kamuwa da cutar da shaye shayen magungunan kawar da cutar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne NCDC ta bayyana adadin yawan mutanen da kasar nan ta rasa a dalilin kamuwa da wannan cuta a 2018.

Rahotan ya nuna cewa mutane 559 sun kamu da cutar inda daga ciki mutane 143 suka mutu a jihohi 22 tsakanin watannin Janairu zuwa Nuwambar 2018.

Matakan da NCDC ta dauka sun hada; Hada hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), ma’aikatar aiyukkan noma da ci gaban karkara, ma’aikatar muhalli, da hukumar hana yaduwar cututtuka na kasar Amurka domin karfafa bincike da kula da wadanda suka kamu da cutar.

Hukumar ta bude wurare don samarda kula na gaggawa wa duk wadanda suka kamu da cutar. Sannan kuma a yanzu haka wuraren yin gwajin cutar sun karu zuwa hudu a kasar nan.

A karshe ministan kiwon lafiya ya bayyana wasu hanyoyi biyar da za su taimaka wajen kare mutane da ma’aikatan kiwon lafiya daga kamuwa da zazzabin lasa.

Ga hanyoyin

1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.

2. Ya ce duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.

3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci neasa da fitsari da kuma kashin beraye.

5. Ya ce ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.

Share.

game da Author