Sakamakon binciken wasu likitoci dake jami’ar Khon Kaen a kasar Thailand sun bayyana cewa yawan amfani da na’ura mai kwakwalwa wato komfuta da wayar tafi da gidan ka na iya kawo ciwon wuya da na sauran gabobin jiki.
Likitocin sun gano haka ne a wata bincken da suka gudanar a jikin wasu matasa masu amfani da na’urori irin haka guda 30 masu shekaru 18 zuwa 25.
Jagoran binciken Suwalee Namwongsa ya bayyana cewa da dama daga cikin matasan sun kamu da ciwon wuya saura kuwa na fama da ciwon baya duk a dalilin amfani da na’urorin.
” Hakan na yiwuwa ne saboda rashin kula da yadda ake zama ko kuma tsayuwa yayin da ake amfani da na’urorin”.
Bayan haka likitocin sun kuma gano cewa ana iya kamuwa da cututtuka kamar su mura, kwalara da sauran su a dalilin rashin tsaftace hannu da wayar da ake amfani da.
A dalilin haka likitocin ke kira ga matasa da su guji yawan amfani da waya na tsawon lokaci saboda samun lafiya mai nagarta.
Sun kuma yi kira ga iyaye da su rika kwaban ‘ya’yan su su rahe yawan amfani da wadannan na’urorin ganin cewa yin haka na cutar da kiwon lafiyar su.