Amfanin ridi 13 ‘Sesame seed’ a jikin ‘Dan Adam

0

Ana noman ridi matuka a Najeriya sannan mutane na amfani dashi wajen yin abubuwa da dama musamman wajen yin abinci da sauran su.

Da dama na da masaniya game da ridi sai dai yadda suke amfani da ita ne ya banbanta.

Ana amfani da ridi wajen ci haka kawai da suga ko kuma da gishiri. Wasu kan hada shi don maganin bakon dauro a yara da sauran su.

Likitoci yi kira ga mutane da su rika cin ridi don amfanin da yake da shi a jikin mutum.

Ga amfani Ridi

1. Ridi na rage cutar siga wato ‘Diabetes’

2. Yana taimaka wa masu fama da ciwon ido.

3. Ridi na taimakawa wajen nika abinci a cikin mutum.

4. Yana rage kiba a jiki

5. Yana kuma kawar da cututtukan dake kama zuciya.

6. Ridi na maganin Asma.

7. Ridi na dauke da sinadarin Iron dake taimakawa wajen kawar da cututtukan dake kama jini.

8. Yana dauke sinadarin Folic Acid dake taimakawa mata masu ciki da dan dake cikin su.

9. Ridi na karfafa karfin kashi.

10. Yana kawar da cututtukan dake kama fata kamar su kuraje kuma yana hana tsufa da wuri.

11. Ridi na inganta hantar mutum.

12. Yana taimakawa maza da mata wajen saduwa.

13. Yana maganin bakondauro ga yara.

Share.

game da Author