” Irin wadannan ‘yan siyasa, aljihun su kawai ne a gaban su ba mutuncin su da na iyalan su ba.” Wannan shine irin Kalaman da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya rika yi a lokacin da ya samu labarin sauya sheka da wani dan gaban goshin sa kuma tsohon kwamishina a jihar yayi a garin Kazaure.
Baba Santali ya bayyana sauya sheka daga PDP zuwa APC ne a inda ya karbi katin zama dan jam’iyyar APC a mazabar sa dake Kazaure.
Santali na daga cikin wadanda Sule Lamido ke bugan kirji da a jam’iyyar PDP kafin ya fice daga jam’iyyar zuwa APC.
Ya rike ma’aikatan ayyuka na jihar na tsawon shekaru 8 a lokacin mulkin Lamido.
Santali ya ce ya dade yana tare da Buhari a zuciyar sa duk da yana jam’iyyar PDP, amma yanzu ya gamsu matuka cewa jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya fi dacews da shi ba PDP ba.
” Za mu hada hannu da gwamnatin jihar karkashin gwamna Muhammad Badaru domin ganin Buhari ya lashe zabe mai zuwa.
Shiko Sule Lamido cewa yayi dama can haka irin su suke, sun fi gane wa su cika aljihun su a maimakon mutuncin su da na iyalan su.
Ya ce duk da kaucewa da wasu suke yi zuwa jam’iyyar APC, PDP za ta yi raga-raga da APC a jihar, yana mai cewa mutanen jihar sun gane kuskuren da suka yi na zaben APC a 2015.