Yadda tirela dauke da lodin shinkafar kamfen din APC ta markade mutane 45

0

Jiya Asabar ta kasance bakar rana ga al’ummar garin Iworoko Ekiti, yayin da wata motar Dangote makare da shinkafa ta tattake jama’a da dama.

Jami’an ‘yan sanda ko na kiyaye hadurra ba su bayyana adadin mutanen da suka mutu ba, amma dai wadanda suka gane wa idon su gawarwakin sun ce mamatan za su kai 45.

An yi lodin shinkafar ce mai dauke da tambarin APC, mallakar dan takarar sanatan jihar Ondo, Tayo Alasoadura.

Alasoadura sanata ne mai wakiltar Ondo ta Tsakiya, wanda ke takarar sake komawa kan mukamin sa a zaben 2019.

Ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa akalla ya ga gawarwaki 45, wadanda suka mutu yayin da tirela din mai dauke da shinkafa ta murje wata karamar mota mai dauke da fasinjoji, sannan kuma ta kwace wa direban, ta afka cikin kasuwa.

An ce burki ne ya tsinke wa direban motar a garin na Iworoko, gefen Ado-Ekiti a jihar Ekiti.

A garin ne dubban daliban Jami’ar Jihar Ekiti ke zaune.

Wani da ya ga yadda aka rika rika jigilar gawarwakin mamata, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya ga motocin daukar gawa masu yawa su na ta jigilar mamatan zuwa asibiti.

Wani da abin ya faru a idon sa, ya ce hadarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Asabar.

“Motar na dauke ne da lodin shinkafa wadda aka yi wa tambarin hoton fastar dan takarar sanatan APC na jihar Ondo, Tayo Alasoadura. Wato burki ne ya tsinke. Mutane 45 na gani sun mutu, kuma ba su ke nan ba.”

Mutanecda yawa ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose duk sun jajanta kuma sun mika ta;aziyyar su.

Share.

game da Author