‘Yan takarar da suka fafata neman kujerar gwamnan jihar Neja a inuwar jam’iyyar PDP duk sun canja sheka zuwa jam’iyyar APC.
‘Yan takaran sune, Ahmed Ibeto, Hanafi Sudan, Ahmed Baka, da Umaru Ahmed da aka fi sani da Dogon Koli.
Ahmed Ibeto da ya yi magana a madadin masu canja shekar ya ce za su maida hankali wajen ganin jam’iyyar APC ce ta lashe zabe mai zuwa a kowani mataki a jihar.
A nashi jawabin, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jinjina wa gwamnan jihar ne, Abubakar Bello, inda yace matashi ne da ya taka rawar gani a jihar.
Osinbajo ya yi kira ga mutanen jihar da su tabbata sun sake yi wa Bello ruwan kuri’u a zabe mai zuwa domin ci gaba da kwankwadar romon dimokradiyya a jihar.
Gwamna Bello, kira yayi ga mutanen jihar da su tabbata sun adana katin zaben su kusa sannan su fito kwan su da kwarkwata su zabe jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Darektan Kamfen din Shugaba Buhari Rotimi Amaechi ya roki mutanen jihar Neja da su tabbata sun zabi APC a zabe mai zuwa.
Discussion about this post