ZAMFARA: ‘Yan sanda sun yi kamen wasu 23 dauke da bindigogi da suka saje da masu zanga-zanga

0

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Zamfara Usman Belel ya bayyana wa manema labarai cewa jami’an ‘yan sanda sun yi kamen wasu dauke da bindigogi da suka saje a zanga-zangar garin Tsafe, jihar Zamfara, suka kona motoci da wasu ofisoshi a sakatariyar karamar hukumar Tsafe.

Idan ba a manta ba, a safiyar litinin ne wasu matasa suka tattare manyan titunan da ya ratsa ta garin Tsafe suna zanga-zangar nuna fushin su ga rashin tsaro da ya addabi mutanen jihar.

Sai dai kuma Kwamishina Belel ya bayyana cewa a dalilin wannan zanga-zanga wasu da ba asa ko su waye ba a lokacin dauke da bindigogi suka saje da masu zanga-zanga suka nemi tada hankalin mutane a garin na Tsafe.

” Wadanda suke zanga-zanga daban, sannan wadanda suka shigo cikin su don tada zaune tsaye daban.

” Wasu ne da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijra suke zanga-zangar a maida su garuruwan su, kawai sai irin wadannan matasa ‘yan taratsi suka shige cikin su suka fara harbe-harbe da bindigogi kafinnan suka far wa sakatariyar karamar Hukumar Tsafe.

” Sun banka wa ofishin shugaban karamar hukumar wuta sannan suka kona motoci da dama dake wannan sakatariya.

Belel ya kara da cewa wadanda aka kama su 23 na nan tsare a hannun ‘yan sanda kuma ana nan a na zurfafa bincike domin kamo sauran da suka arce.

Share.

game da Author