MATSALAR TSARO: Zanga-zanga ya barke a jihar Zamfara

0

Mutanen jihar Zamfara sun tare babban titin Gusau zuwa Abuja-Kaduna-Kano domin nuna fushin su ga yadda mutanen jihar ke fama da ayyukan ta’addanci, fashi da yin garkuwa da mutane.

Mutane musamman Mata da Matasa ne suka yi cincirundo a titunan inda suke ta ife-ife suna sukar gwamnatin jihar da na shugaba Muhammadu Buhari bisa gawar samar da zaman lafiya da ta gagara yi.

Shidai wannan zanga-zanga ya faro ne da tare hanyoyi amma zuwa yanzu da muke ruwaito muko wannan labari tuni har an banka wa sakatariyar karamar hukunar tsafe wuta. Sannan kuma duk sun kareraya hotuna da fastocin Buhari da na gwamnan jihar da aka lillika a garin da babban titin.

Kamar yadda wani da abin ke aukuwa a idon sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES, ya ce abubuwan dake faruwa a jihar ya dabaibaye sannan ya addabi mutanen jihar ne da kowa yaga sai fa sun fara irin haka kila daga nan gwamnati ta karkato ta duba su.

Jihar Zamfara dai ta fada cikin mawuyacin hali a shekarun nan inda ayyukan mahara ya addabi mutanen jihar babu kakkautawa.

Mutane da dama sun rasa ‘yan uwa da aminan su a dalilin hare-haren ta’addanci da Mahara ke kaiwa kauyukan jihar Zamfara.

Wannan salo na ta’addanci ya na neman ya gagari gwamnatin Najeriya domin a kullum wayewar gari sai kaji sanarwar ko anyi garkuwa da wasu ko kuma an far wa kauyuka.

Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali dan asalin jihar Zamfara ne kuma ma a karamar hukumar sa ne hare-haren yafi yin tsanani.

Saidai kuma zaman sa na ministan tsaro baiyi wa jihar tasirin komai ba domin kuwa duk da zaman sa haka ba a iya yin hubbasan ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar ba.

Abin takaici ma shine yadda a karamar hukumar sa ne wato karamar hukumar Birnin Magaji wannan ta’addanci yafi yin tasiri inda a kusan kullum sai kaji an fatattaki mazauna wani kauye dake jihar.

Akwanakin baya, minista Dan-Ali ya bayyana cewa rashin iya mulki na gwamnan jihar ne wato Abdul-Aziz Yari ya sa wannan ta’addanci yaki ci yaki cinyewa. Ya zargi gwamnan da nuna halin ko-in-kula da yake yi game da tsaron jihar da mutanen ta.

Share.

game da Author