SUNAYE: Jihohin da suka fi yawan matasan dake neman aikin ‘Yan sanda

0

Hukumar Kula da Ayyukan dan sanda ta Kasa, PSC, ta bayyana karbar takardun fam na neman aikin dan sanda wadanda matasa har 158,773 suka cika.

Hukumar ta bayyana cewa duk da an yi sanarwar cewa ‘yan sanda 10,000 kacal za a dauka, matasan 158,773 sun cika fam-fam din ne a cikin kwanaki 18 kadai da fara cikia fam din.

Kwanan baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kara daukar sabbin ‘yan sanda 10,000 domin a kara inganta tsaro a kasar nan.

Daga cikin wadanda suka cika fom din, 140, 902 duk maza ne, sai kuma akwai mata 17,871.

Jihohin Neja da Kano da Katsina da Bauchi da Kaduna da Adamawa ne suka fi yawan wadanda ke neman shiga aikin dan sanda.

Jihohin Lagos, Ebonyi, Anambra, Abia da Imo ne masu karancin wadanda ke sha’awar shiga aikin dan sanda, inda a wadannan jihohi babu inda matasa 1000 suka cika fam.

Share.

game da Author