Wakilan Kungiyar Malaman Jami’ao’i ta Kasa, ASUU, sun fice daga taron neman yadda za a shawo kan malaman su janye yajin aiki da suka fara tun farkon watan Nuwamba.
Sun fice wa tawagar wakilan da Gwamnatin Tarayya ta tura din ne a karkashin Ministan Kwadago da Ma’aikata, Chris Ngige, a dakin taron jiya Litinin a Abuja.
Sau shida kenan ana zama tsakanin malaman da gwamnatin tarayya tun bayan da su ka shiga yajin aiki a ranar 4 Ga Nuwamba, 2018.
An dai shirya za a gudanar da taron ne da karfe 5 na yamma daidai.
Wakilan Kkungiyar Malaman Jami’o’i sun isa wurin tun kafin karfe 5 na yamma din, amma kuma babu wakilan gwamnatin tarayya ko daya a wurin.
Sai karfe 6 daidai ne Ministan Kwadago Ngige ya isa. Amma kuma Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu bai je ba har zuwa lokacin da malaman suka fusata suka fice daga zauren taron.