Sojojin Najeriya sun fasa korar UNICEF daga Arewa maso Gabas

0

Sojojin Najeriya sun bada sanarwar fasa korar da suka yi wa hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta UNICEF daga yankin Arewa maso Gabacin Najefiya.

Sun janye wannan sanarwa ce awanni kadan bayan jaridar PRNigeria mai kusanci kuma wadda ita ce kamfanin dillancin labaran dukkan hukumominn tsaron kasar nan.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Sojojin Daheriya, Onyema Nwachukwu ne ya bayar da waccan sanarwa ta farko, inda ya bayyana dalilin korar jami’an hukumar UNICEF, ya na mai cewa:

“Dakatarwar da aka yi musu ta zama dole, domin tuni suka karkata daga aikin da aka san su da shi na taimako da ayyukan jinkai ga kananan yara, suka koma su na horas da wasu zababbun mutanen da ke musu aikin kawo wa ayyukan yaki da ta’addanci cikas.

Ya kara da cewa su na kuma yawan zargin sojoji da aikata ayyukan cin zarafin jama’a.

Sai dai kuma ba a sani ba ko sojoji sun samu amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ne kafin su kori UNICEF, domin ba su da wannan ikon na korar ta su.

Hukumar sojoji sun kuma zargi irin wadannan kungiyoyi da yin kalamai da furuci da zarge-zargen da za su iya sare wa sojoji guiwa, wadanda ke sadaukar da rayuwar su wajen dakile ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

SOJOJI DA UNICEF ZA SU SASANTA – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa a yau Asabar za a yi zaman sasantawa tsakanin Hukumar Sojojin Najeriya da kuma UNICEF.

Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a lokacin PREMIUM TIMES ta tambaye shi abin da ake ciki dangane da korar da sojoji suka yi wa UNICEF.

Dukkan zarge-zargen da sojoji suka yi wa UNICEF dai ba su bayar da wasu kwararan hujjoji ba.

Shehu ya ce bangarorin biyu za su zauna a yau Asabar domin su fahimci junan su.

Share.

game da Author