MATSALAR TATTALIN ARZIKI: Gaskiya ta fito daga bakin Buhari, Daga Ashafa Murnai

0

Ranar Juma’ar nan da ta shige ce Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa daukacin gwamnonin Najeriya gaskiyar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, inda ya ce musu a gaskiya ya na cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Buhari ya ce kafin a tayar da komadar da ta komadar da tattalin arzikin kasar nan, sai an yi da gaske, kuma su ma gwamnonin sai sun tashi tsaye wajen tsuke bakunan aljihun su.

Fitowar wannan furuci daga Buhari ta bai wa jama’a da dama mamaki. Akwai wadanda ke kallon cewa tuni Najeriya ta hau saitin zama kasaitacciyar kasa, kamar yadda milyoyin magoya bayan Buhari ke ta kururuwar cewa tattalin arzikin kasar nan ya dawo.

Sannan kuma akwai masu kallon cewa farfaganda ce kawai gwamnati da magoya bayan ta ke yi, da ita kan ta gwamnatin da masu yarda da abin da ta fada ke cewa tattalin arzikin kasar nan ya dawo.

Sai dai kuma furucin da Buhari ya yi wa gwamnoni, wanda Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, ya warware duk wata farfaganda da rufa-rufar da gwamnati da mukarraban ta ke yi wa ‘yan Najeriya cewa tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa.

RANAR WANKA….

Dama idan banda Najeriya, a wace kasa ce za a same ka ka na sayen litar man fetur naira 87, washegari a maida maka ita naira 145, jibi kuma a ce maka tattalin arzikin kasa ya inganta, kuma kai har ka yarda?

In banda Najeriya, ta ya za a same ka ka na canjin dalar Amurka a kan naira N190 zuwa N200, a wayi gari dala daya ta koma N365, kuma shekara uku kenan, tunda ta hau ba ta sauko ba, sannan kuma a ce maka tattalin arzikin kasa ya inganta, kai kuma ka yarda?

Shin idan ba a Najeriya ba, wace kasa ce ka na biyan naira N850,000 kudin tafiya aikin Hajji, a wayi gari farashi ya koma N1,500,000, sannan kuma a ce maka rayuwar ka ta inganta, kai kuma ka yarda?

Ka kasa tashi daga garin ku zuwa wani gari daga karfe 8 na dare, a tafiyar da ba ta wuce kilomita 50 ba, sannan kuma ka ce an ci gaba. Wa zai yarda da kai?

Dama idan ba a Najeriya ba, wace kasa ce wadda gwamnonin ta ba su iya biyan albashi, sannan kuma a ce an samu ci gaba kai kuma ka yarda?

Wace kasa ce in ba Najeriya ba, za a rika karrama wadanda ake zargi kuru-kuru da gurgunta tattalin arzikin jihar su da wawurar dukiya da kashe-mu-raba, sannan kuma kai talaka a zo a ce maka an samu ci gaba, kai kuma ka yarda?

Wace kasa ce idan ba Najeriya ba, gwamnati haka kawai za ta shafa wa allo fenti ta rubuta masa sunan cewa ta kafa sabon kamfani, ku kuma ku yi tsalle ku na murnar kun ci gaba, kai ka ce ana murnar bukukuwan Sallah da Kirsimeti?

Wace kasa ce idan ba Najeriya ba, abin da ku ke saye daga kasashen ketare ya nunka farashin sa, sannan kuma a ce muku tattalin arziki ya inganta, ku kuma ku yarda?

Idan ba Najeriya ba, a wace kasa ce ko tsinken sakace ko dutsin goge kaushi za ta samar wa jama’ar ta, sai ta ciwo bashi, kuma a ce maka tattalin arziki ya inganta, kai kuma ka yarda?

Ta ya za a ce tattalin arziki ya inganta alhali babu wani abu guda daya sahihi da za a iya nunawa a ce an gina a wurare kamar Kano, cibiyar kasuwancin Arewa, wanda zai inganta tattalin arzikin yankin?

WA ZAI AMINCE?

Wa zai amince ya shigo Najeriya da dimbin dukiya ya zuba jari, alhali yankin jihohin da ya kamata a inganta sun shiga masifar garkuwa da mutane?

Ba ka iya barin Abuja ko Kano ko Kaduna ka tafi kauyen ku ka kwana, saboda ka na gudun kada masu garkuwa da mutane su ji labarin an yi bako mai sabuwar riga, su kuma su sungume ka. Sannan kuma an ce maka an samu ci gaba, kai kuma ka yarda. Shin karya ce wannan ko yaudara ko kuma rainin wayo?

Ta yaya wasu kamfanoni daga waje za su shigo su kafa masana’antu a lokacin da gwamnati ke cewa ta gama da Boko Haram, alhali ko makaho ya san ba a gama da su ba?

Ta yaya tattalinn arzikin masu karamin karfi zai inganta, alhali bashi ko lamunin kudin noman rani an rika saka siyasa ciki, ana bayar da shi har ga ‘yan siyasa maimakon wadanda ya kamata su rika cin moriyar sa?

Don me kuwa tattalin arziki ba zai shiga kaka-ni-ka-yi ba, tunda an kasa gane alkiblar da yaki da cin hanci ya sa a gaba? Saboda me aka kasa gurfanar da makusanta da na cikin gwamnati, wadanda ake zargi da wawurar bilyoyin kudade kafin su canja sheka?

Ta yaya wasu za su maida hankali su bazama su na gina masana’antu a jihohin da ake ci gaba da garkuwa da mutane, a gefe daya gwamnati ta fi maida hankali wajen tura ‘yan sanda 30,000 kula da zaben da masu kada kuri’a ba su kai milyan daya ba?

Ta yaya tattalin arziki zai inganta a jihohin da kowane gwamna sai dai ya mike kafa ya jira kason ribar man fetur a karshen wata daga Abuja?

Ta yaya rayuwar jama’a za ta inganta alhali asibitoci sai kara lalacewa da rashin likitoci su ke yi. Ta ya za a ce rayuwa ta inganta a gwamnatin da har yanzu sai maras lafiya ko majinyaci ya bi layin awa biyar kafin ya ga likitan da zai duba shi a cikin minti hudu?

Dama ya za a ce mana rayuwa ta inganta mu kuma mu yarda, tunda masu fita neman magani, ganin likita da binciken lafiyar jiki zuwa kasashen waje sai karuwa suke yi, maimakon raguwa?

Ba ka yi amanna da asibitocin Najeriya ba da tsarin ilmin Najeriya da titinan cikin jihohin Najeriya, duk ba ka mu’amala da su. Sannan kuma a bay aka ce ka ce mana Najeriya ta inganta, mu kuma mu yarda?

Ta yaya za a ce rayuwa ta inganta a lokacin da an fi maida hankali wajen sake cin zabe bisa ga magance manyan matsalolin da suka fi shafar talakawa gadan-gadan?

Ta ya za a yi kasashen duniya su dauke mu da muhimmanci, alhali ba mu bin umarnin kotu a kan hukuncin da bai yi daidai da abinda ran mu ke so ba?

Da wace hujja za a ce tattalin arziki ya inganta, alhali har yau masu mulki ba su gamsu da ilmin da suke bai wa ‘ya’yan talakawa ba? Ko kuwa sun fara maida ‘ya’yan su zuwa firamare da sakandare na gwamnati, kamar yadda suka yi alkawari kafin zaben 2015?

Wa ya taba jin masu mulki na kukan hujewar aljifan su? Saboda su dai ba su san tattalin arziki ya shiga taitaiyin sa ba. A karkara da kananan garuruwa nan ne a ke cin kwakwa. Amma yadda fadar shugaban kasa da gwamnoni da sanatoci da mambobin majalisar tarayya suka rika fantamawa a waccan gwamnatin, a yanzu ma haka su ke fantamawa.

Ita kanta siyasar ma da aka ce za a tsaftace, ko wankan-Gwari ba a yi mata ba, ballanatana a wanke ta da soso da sabulu. Shin ko shugabannin APC sun daina yawo da dimbin matasa dauke da makamai ne irin yadda suka rika tsine wa gwamnatin baya, har su na rantsuwar cewa idan sun hau za su kawar da wannan dabbancin?

Na dai yarda an samu ci gaba wajen yawaitar matasan mawaka masu farfagandar yekuwar tallata gwamnati, sai kuma dandazon sojojin baka ‘yan soshiyal midiya wadanda ba su ganin laifin wannan gwamnatin. Sai dare ya raba tsaka, ka gama wakar ka ko tura bayanai a soshiyal midiya, ka daga kai ka kalli sili, ka rasa tuna abinda aka yi wa al’ummar garin ku har rayuwar su ko tattalin arzikin su inganta.

Ka na nan ba da dadewa ba za ka ga wasu sun fito su na cewa Buhari bai ce tattalin arzikin Najeriya ya shiga halin kaka-ni-ka-yi a gwamnatin sa ba.

Mai karatu ka rubuta ka ajiye, wata rana sai ka ce ai kuwa dama na fada.

Share.

game da Author