A taron tattauna hanyoyin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa Najeriya za ta bukaci akalla Naira biliyan 134 domin ganin haka ta faru.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), hukumomin gwamnati da kungiyoyin bada tallafi suka halarci wannan taron da aka yi a Abuja ranar Litini.
Taron ya tattauna tsara ingantattun hanyoyin da za su taimaka wajen samar da kiwon lafiya mai nagarta a Najeriya wanda idan haka ya faru zai taimaka wajen inganta sauran fanonnin dake kasar.
Ihekweazu ya ce tsara wadannan hanyoyi ya zama dole musamman yadda bincike ya nuna cewa aiyukkan kawar da cututtuka da kasar nan ke yi ba abin a zo a gani bane.
” Idan ba a manta ba a kwanakin baya cututtuka kamar su sankarau,shawara,zazzabin Lasa, Monkey Pox, bakon dauro suka bullo a kasar nan inda a dalilin haka mutane da dama suka rasa rayukan su wasu kuma suka galabaita.
” Duk wadannan cututtuka za a iya magance su ta yin allurar rigakafi wanda a yanzu haka gwamnati ta fara yi amma duk da haka akwai sauran aikin da ya kamata a yi game da dakike yaduwar cututtuka.
” Gwamnati za ta iya ware wadannan kudade da ake bukata idan ta kara mai da hankulan ta wajen ganin ta daina yawan dogaro da tallafi daga kungiyoyi.
A karshe jami’in WHO Peter Lasuba ya karfafa gwiwowin gwamnatin Najeriya wajen tanada wadannan kudaden da ake bukata. sannan ya ce cin nasara a wannan burin zai taimaki wajen kawo wa kasar ci gaban da take bukata.