Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa za ta kaddamar da atisaye mai suna “Egwu Eke III – Python Dance” a fadin kasar nan, domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaye kasar nan.
Sun ce sun shirya yin atisayen na game-gari, domin share dattin da zai iya kawo kalubale ga gudanar da zaben 2019, wanda ke ta kara matsowa.
Babban Hafasan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai ne da kan sa ya bayyana haka, a wani taro da manema labarai da ya yi a ranar Juma’a, a Maiduguri.
Ya ce za a fara atisayen a ranar 1 Ga Janairu, zuwa 28 Ga Fabrairu, 2019.
Shekaru tara kenan sojojin Najeriya ke fama da yaki da Boko Haram, sannan kuma sun kaddamar da wani yakin da wasu tsirarun mahara da suka addabi yankin jihar Zamfara da kisa da kuma garkuwa da mutane.
Laftanar Janar Lamidi Adeosun ne ya wakilci Buratai wurin taron manema labarai din.
Ya lissafa kalubalen da ke neman tunkarar zaben 2019 cewa sun hada da: Tsageru na si gaba da tanadar makamai, kakkafa gungiyoyin mahara da kuma hargitsin da ‘yan siyasa ke haddasawa.