‘Yan siyasa na neman mu sayar musu da katin zaben da ba a karba ba –INEC

0

Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC na jihar Oyo, Mutiu Agboke, ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan siyasa na tunkarar hukumar su na neman a sayar musu da katin zabe na dindindin da ke tule a ofishin su, wadanda masu katin har yau ba su je sun karbi abin su ba.

Agboke yay i wannan fallasar a lokacin da ya ke gabatar da jawabin bude taron kwana daya na sanin makama da aka shirya wa masu jaridun ‘online’ a jihar.

Sai dai kuma ya ce babu yadda za a yi a sayar musu da ko guda daya. Ya yi jawabin ne a lokacin da ya ke kara nanata da kuma yin kira ga wadanda ba su karfi katin su na jefa kuri’a ba da su gaggauta zuwa domin su karbi abin su.

Ya ce a zaman yanzu akwai katin zabe na dindindin da ba kai ga karba ba a jihar Oyo kadai har guda 914,529.

Kwamishinan Zaben, wato REC na jihar Oyo dai bai ambaci sunayen wadanda suka yi yunkurin sayen katin ba, amma ya jaddace cewa za a gudanar da zabe mai inganci, kuma sahihi karbabbe a jihar Oyo.

“Ba ni da sunayen su a hannu na, domin ba a ba ni sunayen su ba, domin rahoton da aka kawo mana ba a ce mana ko ‘yan wace jam’iyya ba ne.” Inji Agboke.

Daga nan kuma ya roki ‘yan jarida su tsaya akan tsarin aikin jarida na yi wa kowane bangare adalci, ba tare da buga labarai na son rai ba.

Share.

game da Author