Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa tabargazar da aka yi a karkashin mulkin PDP ta haddasa yunwar da ake ta maganar ana fama da ita yanzu a fadin kasar nan.
Haka Amaechi ya furta jiya Juma’a a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a taron kaddamar da fara kamfen na takarar shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC.
“Ku na fama da yunwa ne saboda sun sace muku kudade. Idan da a ce akwai kudaden, to da ba za ku yi fama da yunwa ba a hanlin yanzu.”
Amaechi wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne, shi ne darakta janar na sake zaben Buhari.
Ya ce babbar matsalar kasar nan ita ce rashawa da ta yi katutu, kuma Buhari ba zai sake ba daga kokarin sa na yaki da cin hanci da rashawa da ya ke yi.
Idan ba a manta ba, Jihar Ribas ta zargi Amaechi da wawure naira bilyan 117 na kudaden da ya saida kadarorin jihar ga wani hamshakin dan kasuwa, Tonye Cole.
An kuma zargi ya yi amfani da kaso mai yawa daga cikin makudan kudaden wajen kamfen din Buhari a zaben 2015.
Gwamnatin Jihar ta yi yunkurin bincikar Amaechi, amma ya kai kara kotu ya roki kada a bincike shi.
Kotu ta ce a bincike shi, amma ya yi ta daukaka karar rashin amincewa a bincike shi, har zuwa Kotun Koli.
Sama da shekara daya kenan, batun na ajiye a kotun koli, ba a sake komawa ta kan sa ba.
Tun 1999 Amaechi ke cikin PDP, har ya yi kwamishina da kuma gwamna na tsawon shekara takwas, a jihar Ribas, jihar da gwamnatin tarayya ta fi dumbuza wa kudade fiye da sauran kowace jiha a kasar nan.