A yau Talata ne kungiyar Hisbah dake jihar Kano ta kama mata 11 da laifin shirya daurin auren mata biyu a matsayin mata da miji.
Wannan abin mamakin ya faru ne a Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge.
Jami’in Hisba Nasiru Ibrahim ya sanar da haka inda ya bayyana cewa sun sami labarin haka ne daga bakin mutanen da suka san aiyukkan da wadannan mata ke yi.
” Mun sami labarin cewa ana daurin auren wasu mata biyu da Safiyya Yobe da Fatima Gezawa a Sabon gari.
Ibrahim yace jin haka ke da wuya suka gaggauta zuwa Sabon gari inda suka kama mata 11 cikin su da mata biyu da ake bunkin daurin auren su a matsayin mata da miji.
Daya daga cikin matan da aka kama mai suna Fati Jaririyar-Zuciya ta bayyana cewa su matan kungiyar rawa ne sannan babu aiyukkan liwadi a kungiyar su.
” Mun ga cewa kamata ya yi shugaban kungiyar mu Fatima Gezawa ta sami mataimakiya inda hakan ya sa muka zabi Safiyya Yobe sannan muke taya ta murna a dalilin nasarar cin zaben da ta yi.”
Bayanai sun nuna cewa auren jinsi daya tsakanin mata a jihar Kano ba sabuwar abu ba ne domin a kwanakin baya Hisbah ta kama wata tantiriyar mace da ake kira Aunty Maiduguri a bukin auren ta da ta yi da mata hudu rana daya.
Bisa ga bayanan ta Aunty Maiduguri ta yi ta ce bukin taya wata tubabbiyar karuwa suke yi a ranan.
Discussion about this post