RAKA TSUMMA JUJI: Yadda kurwar Klopp ta rika fatattakar Mourinho a duk inda ya shige

0

A yanzu korar mai horas da ‘yan wasan Manchester United da ke kasar Ingila, wato Jose Mourinho, ba bakon labari ba ne. Sai dai kuma abin da masu sha’awar kallon kwallon kafa suka manta, shi ne, dukkan korar da aka yi masa a kungiyoyi uku a jere, duk mai horas da ‘yan wasan kungiyar Liverpool ta Ingila, Jorgen Klopp ne musabbabin korar ta sa.

Klopp ya fara haddasa korar Mourinho tun daga kungiyar Real Madrid, inda bayan hikima da dabarar koyar da wasa da kuma rigingimun Mourinho da ‘yan wasa irin su Ronaldo da Sergio Ramos, ya haifar wa Madrid rashin tabuka komai a tsawon lokaci.

An yi juriyar maleji da Mourinho, har zuwa lokacin da kingiyar BRUSSIA DORTMUND ta Jamus, a karkashin mai horaswa Klopp, ta lallasa Mourinho da REAL MADRID da ci 4-1. A lokacin ne aka kori Mouriho daga Madrid.

Mourinho ya koma kungiyar da ya taba koyarwa, wato Chelsea ta London, inda a can ma sanadiyyar cin da Klopp ya yi masa 3-1 ne aka kore shi. Amma kuma ba a karshin Dortmund ba, a lokacin ya koma LIVERPOOL FC ta Ingila ne.

Wannan kora ta uku da aka sake yi wa Mourinho, a kulob din da ya koma, bayan barin Chelsea, wato MANCHESTER UNITED, a can ma Klopp ne ya bi shi ya kara haddasa masa kora karo na uku.

Ranar Lahadin da ta gabata ne Liverpool ta lallasa Manchester da ci 3-1, inda wannan nasara ta sa Manchester ta kara dauwama ta shida a jerin kungiyoyin gasar Premier, ita kuma Liverpool da ta yi nasara a kan ta, ta samu hayewa ta daya a jerin kungiyoyin.

Karin abin haushi a wasan, sai da ‘yan gaban Liverpool suka auna mai tsaron gidan Manchester har sau 36, ita kuma Manchester sau 6 kacal ta auna mai tsaron gidan Liverpool har aka tashi.

An kori Mourinho a daidai lokacin da Manchester United ta buga wasanni 17 a gasar Premier, amma ba ta da kwallaye ko daya. Ma’ana, yawan kwallayen da aka ci ta sun yi daidai da yawan kwallayen da ta ci.

Rabon da kungiyar ta yi irin wannan katabus din kuwa, tun kakar wasan 1990-1991.

Duk ma inda Mourinho zai koma, to ko shakka babu ba taba mantawa da Klopp a rayuwar sa ba. Kuma watakila ko inuwar Klopp ya hanga, zai iya dafe keya ya sheka a guje cikin tsakiyar taron jama’a, don kada su kara yin arba gaba-da-gaba ko a tsakiyar filin kwallo, har kurwar sa ta kama shi.

Mu dai sai mu ce tabbas Klopp ba ya jin kyamar daukar tsumma ya jefar da shi a juji, ko da kuwa tsumman ya na zarnin fitsari!

Share.

game da Author