Dan Majalisar Tarayya wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Harkokin Jinkai da Agaji ga Masu Gudun Hijira, Sani Mohammed ya karyata gwamnatin tarayya cewa karya ta ke zabga wa ‘yan Najeriya, ba ta ci karfin Boko Haram ba.
Ya ci gaba da cewa yankin su dai kam ya durkushe, kuma ya na jin tsoron abin zai shafi sauran yankunan kasar nan.
Sani Dan Majalisar Tarayya ne, kuma dan jam’iyya mai mulki, APC.
Sani ya yi wa abokan aikin sa wannan jawabi ne, bayan ziyarar da ya kai wasu jihohin Arewacin kasar nan. An buga bidiyo na jawabin na sa a gidan talbijin na online, wato Oak TV.
” Ba mu dade da dawowa daga duba-garin ayyuka a jihohin Barno da Yobe ba. Saboda haka maganar cewa ana mamaye da Arewa masu gabas, da Hon. Chika ya yi, kadan ma kawai ya fada.”
“Arewacin kasar nan fa ya kusa durkushewa. Maganar gaskiya fannoni fa yawa fa sai kara tabarbarewa suke yi. To tsoron da na ke ji, shi ne abin nan zai iya shafar sauran yankunan kasar nan.
“Mun je Maiduguri a ranar Alhamis da ta gabata ta. Amma ko kayan mu ba mu gama saukewa ba , sai Boko Haram suka kai wa sansanin masu gudun hijira hari da ke Dalori 2, wanda ke kallon Jami’ar Maiduguri. Suka kone mafi yawan sansanin, suka kashe mutane takwas, suka saci mata suka gudu da su, sannan suka arce cikin daji, ba tare da an bi su ba ko an tare su, an yi gumurzu da su ba.” Inji Sani.
“Mun je Bama, garin da shi ne na biyu a jihar Barno wajen yalwar arziki, domin ya na kan hanyar fita kasashen Chadi, Nijar da Kamaru ne.”
Sani ya ce maganar da gwamnati ke yi wai zaman lafiya ya dawo, an samu kwanciyar hankali, duk karya ce tsagwaron ta kawai.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha cewa ya gama da Boko Haram.
“Kaf a garin Bama ba za ka samu mutane 200 ba zaune a garin ba. Maganar wai tsaro ya samu, zaman lafiya ya dawo a yankin Arewa Maso Gabas, ba gaskiya ba ce, har ma gara sauraren tatsuniya da sauraren wannan kalamin. Karya kawai ake yi.” Inji Dan Majalisar Tarayya Sani.
Daga nan sai ya goce ya fara bada labarin yadda suka karke a ziyarar gani da ido da suka kai Barno da Yaobe, ya na cewa:
“Kafin a yarda a raka ka yankunan da muka je, sai ka samu rakiya gungun gaggan sojoji masu yawa. Su kan su sojojin, duk da kwarin guiwar da muka ba su, magana ta gaskiya ita ce zuciyar su a karye ta ke.
“Mun zarce mun ce Gashuwa a jihar Yobe a ranar Asabar. A kan hanyar mu ta komawa Maiduguri da misalin karfe bakwai na dare, mun kasa shiga Maiduguri, wadda tazarar ba ta kai tafiayar awa daya ba, a lokacin da bakwai na dare ya yi mana a hanya. Tun daga karfe shida na yamma har zuwa yanzu, babu mai fita a cikin Maiduguri. Ina mamakin yadda abokan aiki na ba su bayyana gaskiyar abin da ke faruwa a zauren majalisa domin kowa ya ji.
“Sai dai muka tirje a Damaturu, daga mu sai kayan da muke sanye, babu tawul na wanka ko barushin goge baki, har sai washegari lokacin da aka ba mu hanyar shiga garin mu da jami’an tsaron da ke mana rakiya.”
Mohammed ya ce kwamitin su ya kasa isa garin Chibok, saboda rashin tsaro a kan hanyar tafiya.
“Daya daga cikin dalilin ziyarar mu Barno, har da zuwa garin Chibok. Amma maganar gaskiya duk wanda ya ce zai je Chibok, to sai dai a tsinci gawar sa a kan hanya. Domin kwanaki uku kacal da suka gabata, Boko Haram sun je har mahaifar Hafsan Hafsoshin Sojoji, Tukur Buratai, su ka kashe mutane, kuma babu wanda ya tunkare su.
“Maganar gaskiya ita ce Boko Haram din nan dai suna rike da wasu yankunan da su ke ne mulkin su.” Inji Honarabul Sani.