Kalmar makwabtaka kalma ce da ta samo asali daga Kalmar makwabci, wato mutumin da kuke zaune waje daya dashi a unguwa ko a wajen sana’a (kasuwa, wajen aiki).
Kafin zuwan musulunci kasar Hausa, Bahaushe bashi da wani alaka da yake nufin makwabtaka kamar yadda take yanzu. A wancan lokacin abun da Bahaushe ya ke amfani dashi wanda yayi kusa da makwabtaka shine zaman gandu.
Zaman gandu zama ne wanda uba da matayen shi da yayan shi da matan yayan shi da kannin shi da matan kannin shi da duk wanda yake da alaka dashi ta mazantaka suke zaune a gida daya kuma maigida ne yake da alhakkin ciyar da su da yi musu tufafi da basu tsaro da dai sauran su.
Haka duk wanda yake zaune a karkashin maigidan dole ne zai bishi wajen sana’arshi ya kuma sa hannu domin taimakawa maigidan.
Bayan zuwan musulunci kasar Hausa da kuma karbar da bahaushe yayi wa musulunci sai Kalmar makwabtaka ta samo asali. Da yake bahaushe mutum ne wanda addinin musulunci yayi tasiri akan dukkanin al’adunsa, dole ya mayar da makwabtaka ta zama daya daga cikin muhimman al’adunsa.
A addinance, makwabtaka na nufin zaman amana da taimakon juna tsakanin mutane da suke zaune a unguwa daya ko wajen aiki ko sana’a. alaka ce wadda take rikidewa ta koma yanuwantaka ta yadda magindanta suke bibiyan al’amuran wadanda suke tare.
A da, makwabta tare suke cin abinci, tare a ke yiwa yara kaciya da kai su makaranta. Irin wannan makwabatakar
ce ta sa hausawa a wancan lokacin su ka zauna cikin aminci da lumana. Makwabataka a musulunci ta na daraja har kasha uku kamar haka:
1. Makwabci Musulmi, makusanci (Dan-uwa): Shi wannan yana da hakkoki uku, hakkin Musulunci ga hakkin makwabtaka, ga kuma hakkin ‘yan uwantaka.
2. Makwabci Musulmi: shi wannan yana da hakkoki biyu ne kawai, wato hakkin makwabtaka, sai kuma hakkin Musulunci.
3. Makwabci wanda ba musulmi ba: shi ma nan yana da hakki daya ne kawai wato hakkin makwabtaka.
Tsare wadannan hakkoki da muka bayyana ya yi tasiri kwarai wajen samun kyakkywar dangantaka ba kawai tsakanin bahaushe da danuwansa ba, dangantaka ce wadda ta tsare mutumcin har wand aba musulmi ba.
Daga cikin amfanonin makwabtaka akwai kyautatawa makwabci ta hanya kula da iyalanshi in yayi tafiya, aika mai da tsaraba lokacin da ka dawo daga tafiya, kokarin kaucewa cutar dashi ko ta wace hanya, kare mutumcinsa da dai sauransu.
Makwabtaka a yau gaba daya ya canza inda yawancin magidanta, bama kamar a manyan birane, basu san waye yake makwabtaka da su ba ballantana har su kai da sauke hakkokinsa da yake kansu.
Al’adar cin abinci tare ta kai. A yau kowa ba a bin da ya sani in ba harkar iyalansa ba. Da yawan magidanta basu san ko makwabcinsu yana da abinci ko bashi da shi ba, taimako tsakanin makwabta ya zama tarihi kamar yadda kare mutumcinsu da kaucewa cutar da su ya zama sai wane da wane.
A halin gaskiya, da mutane zasu san mene ne amfanin makwabtaka da ba za suyi sakaci da ita ba. Da yawan abubuwan marasa dadi da muka samu kan mu ciki na tabarbarewar tarbiyya, shaye- shaye, rashin tsaro da sauransu sun kunno kai ne a sanadiyyar lalacewar wannan kyakkyawar al’adar.
Nura Ibrahim, Department of Information and Media Studies, Bayero University, Kano.