Barci hutu ne da jiki ke bukata musamman idan an gaji. Sai dai da dama cikin mutane basu cika maida hankali wajen ganin sun samar ma kan su isasshen barci yadda ya kamata ba.
Rashin samun barci na hana jikin mutum iya nika abinci, dakile kaifin kwakwalwa, rashin karfin a jiki da makamantan haka.
A binciken da farfesa Eve Van Cauter na jami’ar Chicago dake kasar Amurka ta yi, sakamakon ya nuna cewa rashin samun isasshen barci na rage karfin mazakutan maza.
Ta bayyana cewa ga duk namijin da ya saka damuwa, tunane-tunane da hana kan sa barci, zai iya yi masa illar da hatta haihuwa ma zai yi masa wahala.
Cauter ta bayyana illolin da rashin barci ke yi wa jikin mutum kamar haka:
1. Rashin barci na hana karfin mazakutan maza.
2. Yana kawo cutar hawan jini
3. Rashin isasshen barci na kawo ciwon siga wato Diabetes
4. Yana kawo rashin karfi a jika.
5. Yana hana namiji cin abinci.
6. Ta kuma ce a wasu lokuttan mutum kan kara kiba wanda duk alamu ne shima na rashin samun barci yadda ya kamata.
A dalilin haka take kira ga maza da su guji hana kansu barci saboda illolin dake tattare da haka.