ANA WATA GA WATA: Malaman Manyan Kwalejojin Fasaha sun fara yajin aiki

0

Malaman Manyan Kwalejojin Fasaha na Najeriya baki daya sun fara yajin aikin da suka ce ba za su daina ba, har sai an cika musu alkawurran da gwamnatin tarayya ta daukar musu ba ta cika ba.

Kungiyar ta ASUP sun ce akwai wani kwantai na alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi musu tun cikin 2009, da kuma lodin wani alkawarin da aka yi musu cikin 2017 a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari da har yau ba a cika musu ba.

A zaman yanzu dai malaman na kwalejojin ‘Polytechincs’ na kasa baki daya, sun bi sahun ‘yan uwan su malaman jami’o’in Najeriya da suka fara yajin aiki tun ranar 4 Ga Nuwamba, 2018.

Shugaban ASUP na kasa, Usman Dutse, ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa gwamnatin tarayya ta gayyaci shugabanin kungiyar taron neman mafita da za a zauna a ranar 17 Ga Disamba.

Sai dai kuma ya ce wannan bai hana su tsunduma fara yajin aikin ba.

Ya ce za a gani ko a ranar da za a zauna da gwamnati za ta cika alkawurran ko kuma za ta kakare ne, yadda su kuma za su zarce da yajin aikin kai-tsaye.

Kafin su tsunduma cikin yajin aikin da suka fara a yau Laraba, sai da suka bayar da gargadi na kwanaki 21 tun a ranar 2 Ga Oktoba, daga nan kuma su ka kara wa’adin zuwa cikin Nuwamba. Amma ko a lokacin ba su shiga yajin aikin ba, sai a yau Laraba.

Share.

game da Author