El-Rufai ya kaddamar da Kamfen a Kaduna

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya kaddamar da Kamfen din neman zarcewa zango na biyu a Jihar ranara Laraba.

An gudanar da taron ne a filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna.

Da yake jawabi ga dandazon magoya bayan jam’iyyar, El-Rufai ya bayyana cewa idan ya lashe zabe a 2019 zai ci gaba da ayyuka kamar yadda gwanatin sa ta fara.

El-Rufai ya ce gwamnatin sa ta yi rawar gani a tsawon shekaru uku da suka wuce kuma hakan shine babban dalilin da zai sa mutane su sake zaben sa a karo na biyu.

Bayan haka a wannan taro an mika wa duka ‘yan takarar jam’iyyar da suka yi nasara a zabukan fidda gwani Tuta.

Darektan shirye – shirye Sani Bello ya yi kira ga mutanen Kaduna da su tabbata sun zabi gwamna El-Rufai ya na mai cewa PDP ta daba wa kanta wuka zaban Isah Ashiru da ta yi a jihar.

Ya ce ‘yan takarar da jam’iyyar PDP ta tsayar basu cancanta.

Share.

game da Author