Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta rattaba yarjejeniya da Kungiyoyin Masu Motocin Sufuri na Najeriya, NURTW, NARTO da kuma RTEAN, domin hukumar ta yi amfani da motocin su wajen jigilar kayan zabe a ranakun da za a gudanar da zabukan 2019.
Amma kuma INEC da shugabanni da sakatarorin kungiyoyin ne kadai suka rattaba hannun a yau Laraba.
Daraktan Wayar da kai a kan Katin Jefa Kuri’u da Yada Labarai, Oluwole Ossaze-Uzzi, ya ce amma RTEAN ba ta kai ga sa hannu ba tukkuna, saboda saboda wasu dalilan da bai bayyana su ba.
INEC ta bayyana musu cewa za ta bukaci sama da motoci 1000 domin jigila da rarraba kayan zabe.
Ta ce Hukumar Zabe ba za ta iya samar da dukkan motocin zirga-zirgar da ake bukata ba, shi ya sa ta nemi yin amfani da motocin sufuri na haya.
Da ya ke jawabi dangane da dalilin rattaba yarjejeniyar, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ko a shekarar 2015 a lokacin zabe, INEC ta yi amfani da kungiyar direbobi ta NURTW, amma kuma a yanzu ta ga akwai bukatar fadada dangantar cudanyar aikin da saurn kungiyoyin sufuri, domin a tabbatar da an gudanar da jigilar daukar jami’an zabe da kayan zabe zuwa wuraren da za a kai su a kan lokaci.
Yakubu ya bayyana cewa wannan mataki da INEC ta dauka na kara yawan motoci da kungiyoyin sufurin, zai taimaka wajen kara ingancin zaben 2019 fiye da na 2015, wajen kai kayan zabe da jamai’an gudanar da zabe tun kafin lokacin da za a fara gudanar da zabuka a ko’ina.
“Wannan wani nauyi ne da ya wajaba mu sauke shi nan da kwanaki 65 da za fara zabe. Mun mkuma kudiri aniyar ganin cewa an bude kowace rumfar zabe karfe 8 na safe a dukkan fadinn kasar nan.
Ya kuma jaddada cewa INEC za ta rika sa ido a kan motocin da za a yi zirga-zirgar daukar kayan zabe da su, domin tabbatar da cewa ba a karkatar da kayan zabe zuwa wani wuri ko wasu wurare ba.