RIKITA-RIKITAR ZABEN FIDDA-GWANI: An kai INEC kara sau 200 – Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa saboda rikita-rikitar zabukan fidda-gwanin jam’iyyun da aka gudanar a cikin watan Oktoba, masu korafi sun hada da INEC an kai kara har sama da sau 200.

Yakubu ya bayyana haka a ranar Talata a yayin da ya ke gabatar da bude taron lacca a Bikin Yaye Dalibai Karo na 6 a Jami’ar Oduduwa da ke Ipetumodu, jihar Osun.

Ya kara da cewa hukumar sa ta INEC na nan a kan bakan ta na shirya ingantaccen zabe kuma sahihi a 2019.

Ya ce INEC ta na nan ta na ci gaba da gudanar da kyakkyawan shirin ta domin tabbatar da shirya zababbe ingantacce kuma sahihi wanda kowa zai yi amanna da shi.

Sai dai kuma ya yi korafi a kan yadda ake fuskantar kalubalen masu sayen kuri’u, siyasar ko-a-ci-ko-a-mutu, rashin kwakkwarar akidar dimokradiyya a cikin jam’iyyu da kuma rashin iya gudanar da hamayya mai ma’ana a tsakanin jam’iyyu.

Sauran kalubalen da INEC ke fuskanta, sun hada da kalaman haddasa fitina da tsokanar rigima tsakanin ’yan siyasa ko magoya bayan su, rashin tsaro, karfa-karfa da kuma rashin hukunta masu karya dokoki da sharuddan zabe.

Share.

game da Author