Kotu ta ce a ci gaba da shari’ar Dasuki duk da ya ki halarta

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar umarnin a ci gaba da shari’ar tsohon Mai Bada Shawara Ga Shugaban Kasa, Sambo Dasuki, duk kuwa da cewa ya ki halartar zaman kotun na yau Litinin.

Mai Shari’a Ahmed Muhammed ne ya bayar da umarnin a yau, bayan da mai gabatar da kara ya gabatar wa kotu rantsuwar kotu cewa ‘ya rantse da kwansitushin, Sambo Dasuki ya ki zuwa kotu ne domin kawai ya kawo tsaiko ga shari’ar sa da ake gudanarwa.’

PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito a ranar 13 Ga Nuwamba an zauna kotu, amma sai lauyan Dasuki ya karanta wa kotu wasikar da shi Dasukin ya rubuto cewa ba zai sake zuwa kotu ba, domin ita ma gwamnati ta ki bin umarnin kotu cewa a sake shi a bada belin sa, amma kotun ba ta yi komai ba.

A kan haka ne Dasukin ya ce tunda kotu ba ta hukunta gwamnati ba kan bijire wa umarni da kotu ta bayar, shi ma ya bijire wa kotun, ba zai sake zuwa ba, har sai gwamnati ta bi umarnin kotu, ta bayar da belin sa.

A lokacin da aka karanta wasikar, mai gabatar da kara ya nemi mai shari’a da ya ci gaba da shari’a, domin a cewar sa, Dasuki na kawo wa shari’a tsaiko ne kawai.

Sai dai kuma mai shari’a ya ce ba zai yi amfani da bukatar mai gabatar da kara a furuci na fatar baki ba. Ya umarce shi da ya je wata kotu ya rantse da kwansitushin a rubuce, wato ‘court affidavit’ cewa ya rantse da kwansitushin da gangan Dasuki ya ki halartar kotu don ya kawo tsaiko.

Wannan takarda ce da mai gabatar da kara ya gabatar wa kotun a yau Litinin ce ta sa alkalin ya ce to za a iya ci ngaba da shari’a ko da Dasuki bai halarta ba.

Sai dai kuma lauyan Dasuki mai suna Victor Okwudiri, ya tuma tsalle ya ce bai yarda a ci gaba da shari’a ba, domin takardar rantsuwar da mai gabatar da kara, Oladipupo Oluseye ya gabatar, ya cika ta ne ba a bisa hanyar da ta dace kan ka’ida, kamar yadda tsarin doka ta 10 karamin sashe na 1, 2 da 3 suka tanadar ba.

Har Chukudi ma ya buga misali da wani hukunci da Kotun Koli ta taba yankewa a kan wata shari’a tsakanin Sanata Bello Sarkin Yaki da Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da aka yanke hukunci cikin 2015, cewa duk rantsuwar da aka rantse da kwanstushin a kotu, wato ‘affidavit’,
idan ba a bi ka’idar tsarin da doka ta 10 karamin sashe na 1, 2 da 3 suka tanadar ba, to takardar rantsuwar ba ta da bambanci da takardar tsire.

Sai dai kuma duk da hujjojin da lauyan Dasuki ya gabatar, Mai Shari’a ya ce a ci gaba da sauraren karar shari’ar da ya ke wa Dasuki ko da ba ya nan din.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 11 Ga Disamba, 2018.

Tun cikin watan Disamba, 2015 ake tsare da Sambo Dasuki, watan da aka kama Sheikh Ibraheem El-Zakzaky.

Share.

game da Author