An yi kashe-kashe a bukin zagayowar haihuwan wani matashi a jihar Bauchi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa mutane uku sun mutu, gidaje biyu da mota daya sun kone a dalilin bukin zagowar haihuwar wani matashi da aka yi a jihar.

Jami’in halda da jama’a na rundunar Kamal Datti ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES ranar Litini.

Datti ya bayyana cewa wannan abin takaicin ya faru ne a unguwar Yelwa inda garin a hole sai rikici ya barke a tsakanin masu gwangwajewa.

” A dalilin wannan rikici mutane uku sun rasu sannan an kona gidaje biyu da mota daya .”

Ya ce a yanzu haka sun kama mutane 75 da ake zargin suna da hannu a tada wannan rikici.

Datti ya kuma karyata wasu rade-radin da wasu ke yadawa cewa wai rikicin addinine.

Sai dai wasu iyaye mata da ‘yan matan wadannan matasa da ‘yan sanda suka kama sun yi zanga -zanga domin nuna fushinsu da kama matasa 75 din da jami’an tsaro suka yi. Sun koka cewa wadanda aka kama basu cikin wadanna suka tada rikicin.

Wasu mazauna unguwar sun shaida mana cewa har gida wadannan matasa suke bin mutane suna bugewa, sannan su dildila wa gidan fetur su kyasta ashana. Haka kuma wani ma da kwanan sa ya kare an ce make shi aka yi yana kan babur din sa inda nan take ya rasu.

Share.

game da Author