A ci gaba da samar wa matan jihar Jigawa da Tallafi da gwamnatin jihar Jigawa ke yi duk shekara, zata raba wa mata Akuya da bunsuru har 47,544 na tallafi a shekarar 2019.
A shekarar 2018, gwamnatin jihar ta raba wa mata 8,428 akuya da bunsuru har 25, 284.
A badi, wato 2019, za a raba wa mata sama da dubu 15, dabbobi sama da dubu 47 a fadin jihar.
Ya ce wannan tallafi ya na samar wa jihar ribar gaske domin mata na amfani da shi yadda ya kamata kuma ba a samun matsala wajen biyan bashin tallafin.
Bayan haka gwamna Badaru yace kamfanin Dangote na gina kamfanin sarrafa shinkafa a jihar sannan kuma kamfanin Lee na gina kamfani sarrafa rake duk a jihar.