IBRAHIM SAKABA: Yadda kwamandan sojojin da Boko Haram suka kashe ya sha jinjina da gwarzantawa

0

Sojoji da dama abokan aikin Laftanar Kanar Ibrahim Sakaba, Kwamandan Sojojin da Boko Haram su ka kashe tare da wasu sojoji 117, sun jinjina masa tare da gwarzanta shi matuka.

Sun kuma yabi irin jajircewar da sauran sojojin suka nuna kafin a ci karfin su a kashe su a fagen dagar yaki da Boko Haram, wadanda ke karkashin bangaren Albarnawy, wanda ya balle daga rundunar Shekau.

An yi wannan mummunan gumurzu da artabu ne a ranar 18 Ga Nuwamba, a sansanin Bataliyar Sojoji ta 157 da ke Metele da ke cikin jihar Barno, wanda ke kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Chadi.

Gumurzun wanda ya ci rayukan su Sakaba da sauran zaratan sojojin, ya barke ne da misalin karfe 6 na yammacin waccan rana ta Lahadi.

Tun a lokacin dama PREMIUM TIMES ta gano cewa Ibrahim Sakaba ne aka kashe, amma sai ta sakaya sunan sa, tun a ranar Talatar da ta gabata, saboda tubani da kuma jiran gwamnatin tarayya za ta bayyana sunan sa tukunna.

Sai dai kuma sati daya kenan, amma har yau gwamnatin tarayya ba ta bayyana sunan sa ba, kuma har yau babu wata alamar da ke nuna cewa an sanar da iyalin sa da kuma iyalan sauran sojojin da aka kashe halin da ake ciki a fagen dagar da suka rasa rayukan su.

Wani babban jami’in sojan da ya san Laftanar Kanar Ibrahim Sakaba, ya bayyana shi da cewa hazikin soja ne mai kishi, wanda ba ya nuna son kan sa a wurin gudanar da aikin kasa.

“Ai Sakaba din nan ne fa can baya ya ki bin umarnin na gaba da shi, a lokacin da aka ce ya ja ayarin sojoji zuwa yaki da Boko Haram, amma ya ce ba zai ja zugar sojojin Najeriya zuwa makabarta ba, saboda ba su da ingantattun makamai kuma da dama wadanda ke hannun su ma su na bukatar garambawul. Dalilin haka ne har aka hukunta shi.” Inji wannan babban jami’in soja da PREIUM TIMES ta ji ta bakin sa.

An dai tsare Sakaba ne a cikin watan Disamba.

Za a iya cewa saboda jajircewar Bataliya ta 157 da Sakaba ne kwamanda wajen fatattakar Boko Haram a fadeden yankin Metele kusa da kan iyaka da Chadi ne ya sa Boko Haram suka rika yi wa Bataliyar taron-dangi kwanan nan.

Idan ba a manta ba, an kai wa sansanin hari a ranar 8b Ga Oktoba, inda ka kashe sojoji 18, wasu takwas kuma suka ji raunuka. Kuma a lokacin sai da hukumar tsaro ta sojoji ta tabbatar da an kai harin.

Sakaba, wanda aka haifa a ranar 20 Ga Disamba, 1975, an tura shi ne a Barno cikin 2014 a matsayin manjo. Shi ke da lambar daukar aiki soja ta N/10744.

Sakaba ya na da aure, har da dan sa daya.

Ba a dade da tura Sakaba a Maiduguri ba ya yi tankiya shi da M.Y Ibrahim, wanda a yanzu Manjo Janar ne. a lokacin Ibrahim shi ne Babban Kwamandan Riko na Rundunar Sojoji ta 7, inda aka tura Sakaba.

Sanata Bala Na’Allah na daya daga cikin wadanda suka jinjina wa Sakaba da gwarzanta shi bisa cancantar da yi.
Na’Allah ya yi wannan jinjina a zaman Majalisar Dattawa na makon jiya, inda aka dage zaman domin jimamin sojojin da Boko Haram suka kashe.

A na su bangaren, sojojin Najeriya sun ce wadanda aka kashe ba su kai yawan wadanda ake yayata a kafafen yada labarai da soshiyal midiya ba. Amma kuma har zuwa yau sun ki bayyana adadin da suka hakkake an kashe.

Share.

game da Author