Uwargidan gwamnan jihar Kebbi Zainab Bagudu ta koka kan yadda yara musamman ‘yan kasa da shekara biyar a jihar ke fama da matsanancin yunwa.
Zainab ta fadi haka ne a taron wayar da kan mutane game da inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana wanda kungiyar ‘Maternal Newborn and Child Health (MNCH)’ ta shirya kuma aka yi a karamar hukumar Jega.
Ta ce bincike ya nuna cewa kashi 60 bisa 100 na yara kanana a jihar na fama da matsanancin yunwa sannan a Najeriya yara miliyan 11 ne ke fama da matsanancin yunwa.
” A yanzu haka wadannan yara ba su girma yadda ya kamata saboda matsalar , gashi kuma ana jinjina wa jihar wajen noman shinkafa da abinci amma kuma yaran mu na fama da yunwa.
A karshe ta kuma yi kira ga kananan hukumomin jihar da su gina wuraren da mata ma’aikata za su rika garzaya lokaci-lokaci suna shayar da ‘ya’yan su nono.
Discussion about this post