Malaman Jami’o’i sun gindaya sharuddan janye yajin aiki

0

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta gindaya sharuddan da ta ce sai gwamnatin tarayya ta cika tukunna sannan za ta janye yajin aikin da ta fara tun a farkon wannan wata.

Shugaban Kungiyar malaman Abiodun Ogunyemi ne ya furta haka a wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES, jiya Lahadi da dare.

Ogunyemi ya ce abin takaici ne matuka yadda shugabannin Najeriya ke kwan-gaba-baya da kuma dawurwura a wuri daya, sun ki gusawa gaba domin su magance matsalar da ta dabaibaye harkar ilmi a jami’o’in kasar nan.

“Wasu daga cikin wadannan sharudda sun hada da fara aiki gadan-gadan da yarjejeniyar da aka kulla a cikin watan Oktoba, 2017.

“Idan suka fara aiki da abin da wannan yarjejeniya ta kunsa, kuma suka canja tawagar da muke tattaunawa da ita daga bangaren gwamnati, to za mu iya janye yajin aiki, mu koma batun tattaunawa.

Ya kuma nuna cewa lalacewa da tabarbarewar kulawar da gwamnatin tarayya ke wa jami’o’i a kasar ne ya sa malamai ba su kwadayin zuwa koyarwa daga wasu kasashen waje, kuma dalibai daga wasu kasashe ba su zuwa karatu.

Ya ce da ana samun malamai da dalibai, da martabar jami’o’in kasar nan ta karu a idon duniya.

Share.

game da Author