Boko Haram sun banka wa kauye mai suna Mammati wuta, jiya Laraba da dare, kusa da Maiduguri.
Wanda aka kai harin kan idon sa kafin ya arce, ya shaida wa manema labarai cewa hayaki ya tirnike kauyen, kuma da misalin karfe 11 na dare ne maharan suka kai wa jama’ar garin hari.
Ya ce tun ma kafin a Ankara sai dai suka ji harbi na ta tashi sama kawai ko ta ina.
An ce maharan a kan kekuna suka isa kauyen, suka rika bi gida-gida sun a cinna wuta.
Wasu mazauna kauyen wadanda suka rigaya suka kwanta barci da wuri, sun farka firgigi a gigice yayin da suka rika jin ruwan harsasai da karar bindigogi na tashi ko ta ina.
Da yawan su sun bayyana cewa ba don karar harbin da ya tashe su ba, to da sai wuta ta kone su kurmus. Haka Muhammad Mammati ya shaida wa PRMIUM TIMES.
Wakilin mu da ya ziyarci kauyen ya ce ya ga gawarwakin dabbobi birjik wadanda suka kone, kuma ya hatsin da aka kone mai tarin yawa.
Wakilinmu kuma ya ga masu zaman ta’aziyar wani mutum daya da aka kashe.