Gobara ta babbake dakuna shida da shago daya a jihar Kano

0

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ya bayyana cewa gobara ta kona dakuna shida da shago daya a kwatas din Rijiyar Zaki.

Mohammed ya sanar da haka ne da yake ganawa da manema labarai ranar Laraba a garin Kano.

Mohammed yace sun fara gudanar da bincike domin gano sanadiyyar wannan gobara.

A karshe ya yi kira ga mutane da su rika hattara ganin cewa an shiga lokacin hunturu yanzu.

Share.

game da Author