Kungiyar Gwamnonin Najeriya sun bayar da sharuddan da sai an cika su kafin su iya biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi.
Sharuddan da suka gindaya kuwa sun hada da rage ma’aikata ko kuma a kara musu kudaden kason da suke karba daga hannun gwamnatin tarayya.
Shugaban Kungiyar Gwamnoni, Abdulaziz Yari na Zamfara ne ya bayyana wa manema labarai haka jiya Laraba da dare, bayan tashin su daga taro a Abuja.
Yari ya ce sun yanke shawarar nada Kwamiti na Gwamnoni Takwas da za su je su zauna tare da Shugaba Muhammadu Buhari, domin su baje masa matsalolin da jihohin ke fuskanta a faifai.
Gwamnonin sun had a da na: Lagos, Kebbi, Filato, Bauchi, Akwa Ibom, Ebonyi, Enugu da kuma Kaduna
Yari ya kara da cewa kaf a Najeriya jihar Lagos ce kadai za ta iya biyan albashin naira 30,000 mafi kankanta.
Ya buga misali da ita kanta Lagos cewa a yanzu ta na kashe naira bilyan 7 a kowane wata, wajen biyan albashi.
Ya ce idan aka maida mafi kankantar albashi daga naira 18,000 zuwa naira 33,000, Lagos sai ta rika kashe naira bilyan 13 a duk wata kenan.
Discussion about this post