Shugaban kungiyar ma’aikatan kiwon lafiyan da suka kware wajen kula da matsalolin da ya shafi tsufa a Najeriya (GAN) Usaman Ahmed ya yi kira ga gwamnati kan ware kudade domin yi wa tsofaffin kasar nan hidima.
Ahmed ya yi wannan kira ne ganin cewa ire-iren wadannan matsaloli ya faskara a kasar nan.
Ya ce a yanzu haka tsofaffi miliyan tara ne suke a kasar nan sannan babu isassun ma’aikata da wuraren kula da su da gwamnati ta kebe domin su.
” Bincike ya nuna cewa adadin yawan tsofaffin dake kasar nan za su fi haka yawa kafin nan da shekara 2050.”
Ahmed yace kara yawan ma’aikata, kara yawan asibitoci da wuraren kula da tsofaffi na cikin matakan da ya kamata gwamnati ta dauka cikin gaggawa.