An sako daliban makarantar sakandare 78 da aka sace a Kamaru

0

Maharan da suka sace daliban makarantar sakandare 80 a kasar Kamaru sun sako 78 daga cikin su.

Limanin addinin kirista dake kokarin ganin an sako daliban, Samuel Fonki ya bayyana haka ranar Laraba.

Fonki ya ce har yanzu dai da sauran shugaban makarantar da malami daya da suka rage a hannun maharan.

” A kirgan da muka yi maharan sun sace dalibai 80 amma bayan bincike muka gano cewa dalibai 78 ne aka sace tare da shugaban makaranta daya da malami daya.

Fonki ya ce da farko sun zargi yankin Kamaru da ke magana da harshen Turancin Ingilishi da aikata wannan ta’asa amma kakakin bangaren ya musanta haka.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne wasu mahara suka sace daliban sakandare sama da 80 a birnin Bamenda, da ke yammacin kasar Kamaru.

Bayanai sun nuna cewa har ya zuwa jiya Litinin babu wata kungiyar ta’adda ko mahara da ta yi sanarwar hannun ta wajen yin garkuwa da daliban.

An sace daliban ne a cikin yankin Kamaru da ke magana da harshen Turancin Ingilishi, yankin da wasu ‘yan tawaye ke fadan neman ballewa daga kasar.

“An sace mutane 81, ciki har da shugaban makarantar. An tsere da su a cikin jeji.” Inji wata majiyar sojoji.

Rahotanni sun ce an sace dalibai 78, direba daya da kuma wani malami.

Kakakin Gwamnatin kasar ya ce hukuma na bin sawun maganar, amma ba gwamnati ba za ta yi hanzarin cewa komai ba a yanzu tukunna.

Wata jaridar Kamaru mai suna Journalducameroon.com, ta ce mahara sun yi wa sakandare ta Presbyterian Secondary School dirar mikiya, a Nkwem, sannan suka tattara daliban suka arce da su.

An sace su ne a lokacin da suke kokarin rubuta jarabawar fita sakandare ta GCE, inda bayan an gudu da su kuma, maharan suka nuno su a kafar yada labarai ta soshiyal midiya.

Share.

game da Author