Gidauniyar HFAF ta dauki nauyin karatun wasu ‘yan gudun hijira da marasa galihu 38 a Abuja

0

Gidauniyar ‘Hope For All Foundation’ (HFAF) ta dauki nauyin ilimantar da yara ‘yan gudun hijira da marasa galihu 38 a Abuja.

Shugaban kungiyar Alhaja Zainab ta sanar da haka a Abuja inda ta kara da cewa gidauniyar ta zabo yara ne daga sansanonin ‘yan gudun hijiran dake Abuja da wasu marasa galihu dake kauyukan Apo a Abuja.

Zainab ta bayyana cewa gidauniyar ta dauki nauyin biyan kudin karatun yaran, dinka musu rigunan makaranta da kuma takardun karatu.

” Daga cikin yaran da gidauniyyar ta dauka, 14 daga cikin su na aji daya ,18 na aji biyu sannan shida na aji uku na makarantar sakandare.

A karshe Zainab ta ce burin gidauniyyar shine ta dauki nauyin karatun yara miliyan daya.

Share.

game da Author