Dokar hana tattaki a jihar Kaduna na nan daram -Inji Rundunar ‘yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kara jadadda cewa dokar hana gudanar da tattaki ko kuma zanga–zanga a jihar na nan na aiki.

Kakakin rundunar Yakubu Sabo ya sanar da haka wa manema labarai a wata takartada da ta fito daga ofishin sa.

Sabo yace a dalilin haka rundunar ‘yan sandan jihar ba za ta karaya ba wajen ganin ta hukunta duk wanda ta kama da laifin karya wannan doka.

” Muna kira ga mutanen jihar Kaduna da su ci gaba da harkokin su kamar yadda suka saba batare da tsoro ba.

Share.

game da Author