Hukumar Kula Albarkatun Tsaunuka, Tsibirai da Albarkatun Kasa (NGSA), ta kafa tashoshi hudu domin sa-ido da kasa kunnen jin jijjiga da girgizar kasa yankunan Babbabn Birnin Tarayya, Abuja.
Ministan Ma’adinai da Karafa, Abubakar Bwari ne ya bayyana haka a lokacin da ake kaddamar da babbar cibiyar kula da jijjigar kasa da girgizar kasa a Abuja, jiya Talata.
Bwari ya ce an kafa tashoshin hudu ne a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Jam’iar Abuja a Gwagwalada, Jami’ar Veritas a Bwari da Babbar Cibiyar Tashar NGSA, inda can ne babbar tashar ta ke.
Ya ce kayan aikin da aka zuba a babbar cibiyar tashoshin, ba wai kawai za su gano irin nauyin jijjgar kasar ba ce, har ma daidai inda aka yi jijjigar duk na’urori za su iya cafkowa domin a gani, kuma a dauki matakan gaggawa.
Ya ce da farko da tashoshi shida ne aka nemi kafawa a fadin kasar nan, to amma biyo bayan jijjigar kasar da aka yi a Abuja sau biyu a cikin wasu lokuta ba masu tazara ba, hakan ya sa aka yanke hukuncin maida hankali kan Abuja kawai a yanzu.