An kama dagacin da ya yi wuru-wurin cinikin filin naira miliyan 15.5

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun ta bada sanarwar damke Dagacin kauyen Ferowa da ke cikin Karamar Hukumar Ifo, a bisa zargin harkallar naira milyan 15.5 ta kudaden cinikin kantamemen wani fili.

Kakakin ‘yan sandan jihar mai suna Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana haka jiya Talata, cewa sun kama dagacin mai suna Muyideen Folorunsho, bayan wani kamfani ya kai karar sa a rubuce a wurin ‘yan sanda.

“An kama shi ne bayan kamfanin Jaxmat Homes and Properties ya kawo korafi a rubuce cewa dagacin ya yi dillancin sayar wa kamfanin da wani fili mai fadin eka 23 a kan kudi naira milyan 15.5.”

Kamfanin ya rubuta cewa, bayan sun yi ciniki kuma sun biya kudin filin ta hannun dagacin, daga baya kuma sai suka gano cewa ya na kiran wasu mutane ta bayan fage, ya na yanka filin ya na sayarwa ba bisa sani ko iznin kamfanin ba.

Sun ce kafin su farga har dagacin ya sayar da eka 17 daga cikin eka 23 na adadin fadin filin.

Kakakin ya ce Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, Ahmed Iliyasu ne da kan sa ya umarci Sashen Sauraren Korafe-korafe su duba matsalar tare da gurfanar da dagacin kotu.

Bayan an kama shi, dagacin ya amsa cewa ya sayar wa kamfanin da filin, kuma daga baya ya rika kamfatar filaye a cikin makeken filin ya na sayarwa.

Sai dai kuma ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya yanke shawarar kaftar filaye ya na sayarwa ne a daidai lokacin da bikin nadin sa ya gabato, amma ba shi da kudaden da zai yi hidimar shagulgulan biki.

Za a gurfanar da shi kotu da zarar an kammala bincike.

Share.

game da Author