KARIN ALBASHI: Shugabannin Kwadago sun bada wa’adin watan Disamba

0

Kungiyoyin Kwadago sun bayar da wa’adin daga nan zuwa watan Disamba a fara biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, ko kuma su fara yajin aiki na ba ji ba gani, sai ranar da ta kaya.

Sun kuma yi gargadin cewa a kul aka sake aka rage karin mafi kankantar albashin daga naira 30,000 da aka cimma matsaya, a cikin rahoton da aka damka wa Shugaba Muhammadu Buhari.

Baya ga wannan, shugabannin kungiyar sun ce jan-kafa da wani bata lokacin fara aiki da sabon tsarin albashin zai iya haifar da sakamako masar kyau.

Gamayyar Kungiyoyin sun shaida kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sun yi ta faman jiran fara aiki da sabon karin albashin.

Daga nan sun yi kira da a gaggaita mika kudirin ga majalisar domin a yi gaggawar shigar da shi a matsayin dokar da za ta fara aiki ba dadewa ba.

Share.

game da Author