Mahukuntan kasar Indiya sun cafke wasu ‘yan Najeriya biyu, bisa laifin damfarar mutane, ta hanyar watsa tallar karya a soshiyal midiya.
Sun watsa sanarwar cewa su na saida wasu kayayyaki ne a cikin shafin talla na online mai suna Quikr.
Quirk kamfanin tallace-tallace ne a online da aka kafa tun a cikin 2008 a Indiya.
Rahoton da jaridar Tmes ta Indiya ta buda a yau Juma’a, ta ce an kama Samuel Udom mai shekaru 24 da kuma Ngandem Samuel mai shekaru 33, dukkan su da ke zaune birnin Bangalore na Indiya.
Udom ya watsa tallar cewa ya na da Iphone samfurin One Plus 5T na sayarwa. Hakan ta sa wani mai suna Balakrishna Reddy ya tura masa kudi Rupees 82,500, kwatankwacin naira 408,000 a asusun ajiyar sa na banki, amma ya ki tura masa wayar salula din da kuma kyamarar da suka yi ciniki.
Shi ma Samuel an kama shi ne saboda ya zambaci wani mai suna Muhammad Alli Rupees 85,000, kimanin naira 420,000 da ya ce zai sayar masa da wasu kaya.
Amma daga bisani sai aka gano cewa duk bayanan da Samuel ya rika yi, duk na bogi ne kawai, ba gaskiya ba ce.
Discussion about this post